Rajista biyu: ‘Yar takara ta na neman kotu ta hana Bello da APC tsayawa zabe

Rajista biyu: ‘Yar takara ta na neman kotu ta hana Bello da APC tsayawa zabe

Natasa Akpoti mai neman takarar gwamnan jihar kogi ta shigar da wata kara a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja inda ta ke neman Alkali ya haramtawa Yahaya Bello tsayawa zabe.

Kamar yadda mu ka samu labari, an shigar da wannan kara ne a Ranar Litinin, 14 ga Watan Oktoban 2019, inda ake zargin gwamnan da yin rajistar zabe sau biyu; a shekarar 2011 da 2017.

A wannan kara da Natasa Akpoti da shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/122/2019, ta kuma nemi kotun ta hana jam’iyyar APC mai mulki shiga takarar duk wani zabe da za ayi a jihar na shekaru goma.

Lauyoyin Akpoti su na so ya zamana jam’iyyar ba za ta iya shiga duk wata takara da za a yi a jihar Kogi nan da shekaru goma masu zuwa ba. Mike Ozekhome shi ne Lauyan mai wannan karar.

KU KARANTA: Yahaya Bello ya kama hanyar tazarce bayan ya yi sulhu da Abokin adawa

Babban Lauya Mike Ozekhome SAN ya fadawa kotu cewa gwamna Yahaya Bello ya yi rajistar katin zabe sau biyu wanda ya sabawa wani bangaren sashe na 24 na tsarin dokar zaben Najeriya.

Ozekhome ya na ikirarin Bello ya yi takardar zabensa ne a 2011 a birnin tarayya Abuja inda ya sake dawowa jihar Kogi a 2017 ya yi sabon rajitsar katin zabe na PVC don haka ya sabawa doka.

Misis Akpoti ta yi kokarin shiga takarar gwamnan Kogin a karkashin jam’iyyar adawar SDP amma hukumar zabe ta yi waje da ita. ‘Yar takarar ta na ganin cewa INEC ba ta yi mata adalci ba.

Haka zalila Mai tuhumar gwamnan ta nemi takarar kujerar Sanata a zaben 2019 inda shi ma ta sha kashi. Kawo yanzu ba a sanar da kotu za ta saurari wannan kara ba kamar yadda mu ka ji.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel