Babu yunwa a kasar nan, Najeriya na noma abinda za ta iya ciyar da kanta – Nanono

Babu yunwa a kasar nan, Najeriya na noma abinda za ta iya ciyar da kanta – Nanono

Ministan noma da cigaban karkara, Sabo Nanono ya ce Najeriya a noma abinci mai yawan gaske da zai iya ciyar da kasar baki dayanta, sabanin labarin da wasu ke yadawa na cewa akwai yunwa a wasu bangarorin kasar.

Nanono ya fadi wannan maganar ne a Abuja ranar Litinin 14 ga watan Oktoba, 2019 a lokacin da yake cigaba da shirye-shiryen bikin ranar abinci ta duniya wadda za ta kama 16 ga watan Oktoba.

KU KARANTA:An kama wani bakanike ya yiwa yarinya ‘yar shekara 10 fyade a Benue

Ministan ya ce, ko shakka babu kuskure ne mutum ya rinka fadin cewa akwai yunwa a Najeriya. Sai dai kawai ana iya cewa akwai wata 'yar tangarda da gwamnatin tarayya ke kokarin magancewa a karkashin hukumar FAO.

“Daga abinda nake gani cikin dakin taron nan, babu wata alamar yunwa, sai dai masu kiba kawai nake gani wanda ba mamaki wasu kibar tasu ma tayi yawa. Kudurin gwamnatin Najeriya a yanzu shi ne mu rinka noma abinda zamu ci da kanmu.

“Zan iya cewa muna noma abinda zam ci kuma babu yunwa a kasar nan, amma dai idan kuka ce ‘yar tangarda da ba’a rasa ba zan yadda gaskiya. Abinci a Najeriya yana da matukar arha sosai fiye da sauran kasashen duniya.

“A Kano zaka iya cin abinci da naira 30 kacal kuma ka koshi. A ganina kamata yayi mu godewa Allah da ya bamu ikon noma aboncin da za mu iya ciyar da kanmu kuma babu tsada a kasar nan.” Inji Ministan.

Da yake magana akan rufe kan iyaka kuwa, Ministan ya ce, manoman shinkafa da sauran kayan amfani sunyi mirna matuka da rufe kan iyakar. Ya kuma ce duk da cewa mutane da dama ba su ji dadi ba amma abinda ya biyo bayan rufewar labarine mai dadi.

https://dailynigerian.com/nigeria-producing-enough-food-to-feed-itself-nanono/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel