Da dumi dumi: Sojoji sun ceto daliban jahar Kaduna 4 daga hannun yan bindiga

Da dumi dumi: Sojoji sun ceto daliban jahar Kaduna 4 daga hannun yan bindiga

Sauran dalibai guda hudu da wasu gungun yan bindiga suka yi awon gaba dasu daga jahar Kaduna sun tsira sakamakon artabu da aka sha tsakanin dakarun rundunar Sojan kasa da yan bindigan a cikin daji, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi awon gaba da dalibai 14 ne daga makarantar sakandari ta gwamnati dake garin Gwagwada cikin karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Yan Najeriya miliyan 15 ne suke fafutukar neman aikin yi a Najeriya – Gwamnati

Sai dai ba tare da bata lokaci ba Sojoji suka kaddamar da aikin bin sawun yan bindigan, inda a haka suka kubutar da yara 10 daga hannun yan bindigan yayin da suke cikin tafiya dasu a cikin daji.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Sojojin dake aikin tsaro na musamman na Operation Thunder Strike ne suka samu nasarar kubutar da sauran daliban guda biyu a daidai lokacin da yan bindigan suke kokarin tsallakawa jahar Neja ta cikin daji.

Wani daga cikin shuwagabannin al’ummar yankin ya tabbatar da kubutar yaran, inda yace dama Sojoji su dade suna sintiri a yankin, da haka ne suka samu damar bin diddigin yan bindigan, inda suka kai musu harin kwantan bauna.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya ci tura, sakamakon dukkanin layukan wayansa basa shiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel