IGR: Gwamna El-Rufai ya na harin Naira Biliyan 51 zuwa karshen bana

IGR: Gwamna El-Rufai ya na harin Naira Biliyan 51 zuwa karshen bana

Kwanaki wani da kamfain StatiSense su ka yi ya nuna irin kudin da kowace Jihar Najeriya ta iya tatsowa a cikin rabin shekara. A jihohin Arewa dai babu wanda ta iya shan gaban jihar Kaduna.

Daga farkon shekarar nan kawo yanzu, gwamnatin jihar Kaduna ta samu Naira biliyan 22.40. Wannan biliyoyi ba su kai rabin abin da jihar ta ke sa ran samu zuwa karshen shekarar bana ba.

StatiSense ta nuna alamar tambaya game da burin jihar Kaduna na samun kudin shiga na biliyan 51 duk da cewa 44% na wadannan kudi kurum aka iya samu a cikin watanni shidan farkon bana.

Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna cewa babu shakka za su cin ma wannan buri har su zarce hakan a karkashin jagorancin sabon shugaban hukumar KADIRS da ke da alhakin karbar haraji a jihar.

KU KARANTA: Ma'aikatan kananan hukumomi Kaduna sun fara karbar sabon albashi

Mai girma gwamna El-Rufai ya fito shafinsa na Tuwita ne yana cewa “Da yardar Ubangiji, Shugabanmu na KADIRS ‘dan shekara 35 da Ma’aikatansa su na bakin kokarin zarce burin nan.”

Malam El-Rufai wanda ya ke da kokarin tafiya da Matasa ya kara da cewa shugaban na KADIRS ya na da cikakken goyon bayansa da kuma hadin kan mutanen kirkin da ke fadin jihar Kaduna.

Alkaluman da aka fitar da su sun nuna cewa Kaduna ta kerewa jihar Kano wajen tatsar kudin shiga. Har ta kai jihar ta kerewa jihohi irin su Akwa-Ibom kuma ta na kan-kan-kan da Ogun.

Ba da dadewa bane kuma jihar ta tsara kasafin 2020 inda ta warewa manyan ayyuka kashi sama da 70% duk da cewa jihar ta soma biyan sabon tsarin albashin da ya gagari sauran gwamnatoci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel