Bambance Bambance 7 na Aisha Buhari da matan tsaffin shugabannin Najeriya

Bambance Bambance 7 na Aisha Buhari da matan tsaffin shugabannin Najeriya

Sanin kowa ne dan Najeriya wanda ya mallaki hankali da ma sauran al'ummar kasashen ketare masu bibiyar rahotanin kasar nan, Aisha ita ce mai dakin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, wadda ta yi kaurin suna tamkar matan tsaffin shugabannin kasa da suka gabata.

A rahoton da jaridar BBC Hausa ta wallafa, akwai wasu ababe da suka bambata Aisha da sauran matan tsaffin shugabannin kasar musamman wadanda suka fi shahara irinsu Patience Jonathan, Tura 'Yar Adu'a, Stella Obasanjo, Maryam Abacha, da kuma Maryam Babangida.

Ko da yake Hausawa na cewa kowa da irin kiwon da ya karbe shi, hakan ta kasance a yayin da kusan dukkanin matan tsaffin shugabannin kasar sun yi tarayyar kamanceceniyar wasu ababe da dama amma sun sha bamban da Aisha Buhari a wasunsu.

Jaridar BBC ta yi nazari kan abubuwa bakwai da suka bambanta Aisha Buhari da sauran takwarorinta magabata. Bambance-bambance da ke tsakanin Aisha da sauran matan tsaffin shugabannin kasar sun hadar da;

1. Tana sukar gwamnatin mijinta a bainar jama'a kan wasu abubuwa da take ganin ba su dace ba.

2. Sabanin yadda ta kasance a gwamnatocin baya na bude ofishin matar shugaban kasaduk da hakan yana cin karo da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, shugaba Buhari ya rufe ofishin matar shugaban kasar bayan hawansa kujerar mulki. Hakan ya sa Aisha ba ta karfin fada a ji kamar na takwarorinta da suka shude.

3. Aisha ba ta da ta cewa a al'amuran gwamnatin Buhari domin kuwa ba ta da isasshen fada a ji a wurin mai gidanta sabanin takwarorinta da suka shude.

4. Aisha tana takun-saka tsakaninta da dangin miji, musamman yadda rahotanni na baya-bayan nan da suka nuna yadda ake tata-burza tsakanin Aisha da 'dan yayar Buhari, Mamman Daura da iyalansa.

5. Kuruciya

A yayin bincike ya tabbatar da cewa Maryam Babangida da mijinta sun karbi ragamar jagorancin kasar tana 'yar shekara 37, wato kenan ta fi Aisha kananun shekaru, sai dai bambancin zamani na yaduwar kafofin sada zumunta, ya sanya salon kuruciyar Aisha ya bambanta da na sauran takwarorinta da suka shude.

"Aisha akwai kuruciya kuma akwai kyau, kuma wannan kuruciya ta sa ta bambanta da takwarorinta da suka wuce," in ji Rahma Abdulmajid mai sharhi da kuma rajin kare hakkin mata.

Sai dai duk hakan ta kasance, ba za iya zartar da hukuncin cewa Aisha ta yi wa Maryam Babangida zarra ta fuskar gayu ba, kawai dai Aisha ta riski zamanin da aka kara samun wayewa sannan gayu ya kara samun tagomashi a duniya.

6. Jan Aji

Aisha Buhari ta kasance mai akidar zaman daban da sauran takwarorinta na baya, inda ta ke jin kanta a matsayin mace da ba za ta yi rawa da bazar mijinta ba duba da wayewarta da kuma sauyi na zamani da aka samu.

7. Rashin sirranta matsalokin da ke wakana a gidanta

Babu shakka wasu da dama na ganin cewa Aisha Buhari ta bambanta da sauran takwarorinta da suka gabata ta wajen kasa boye abubuwan da ke faruwa a gidanta.

"Duk da cewa dai dama asirin babban gida bai cika rufuwa ba, amma a nata bangaren ana iya karanto cewa tana cike da wata damuwa da lallai ba a san dalilinta ba, sai dai ba za ta rasa nasaba da gidanta ba," in ji Rahama.

"Ko a kwanan nan a hirar da ta yi da manema labarai ranar da ta dawo daga Ingila bayan shafe watanni, an tambaye ta batun jita-jitar auren shugaban, amma sai ta kada baki ta ce ita wadda za a auran ai ba ta fito ta karyata ba.

"Da jin wannan kalami ai ka san cikin kishi irin na mata aka yi shi, kuma ga alama akwai abin da ke damunta mai alaka da gidan aurenta. Ai ba a taba ganin irin hakan a tattare da wata matar shugaban kasa ba.

"Misali Patience Jonathan ai an sha rade-radin cewa mijinta na soyayya da ministarsa Diezani Alison Maduekwe, amma ai duk baram-baramar Patience ba ta taba nuna alama ba. A cewar mai rajin kare hakkin matan.

"Amma mun sha jin cewa ta tabbatar da toshe duk wata kafa da zata bai wa Diezani damar kebewa da mijinta ko cikin sha'anin aiki," kamar yadda Rahama ta bayar da shaida.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel