Majalisar Dattawa ta hautsine kan yadda ake daukan aiki a sirri a manyan ma'aikatu

Majalisar Dattawa ta hautsine kan yadda ake daukan aiki a sirri a manyan ma'aikatu

Ana rade-radin kunnowar rikici a majalisar dattawan Najeriya, a sanadiyar yadda wasu shafaffu da mai cikin sanatoci ke kasafta guraben aiki a tsakaninsu na wasu manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Wasu daga cikin fusatattun sanatocin sun hau kujerar naki ta amincewa da tsarin yadda ake kasafta guraben aiki na wasu manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya a tsakanin shugabannin majalisar dattawan.

Binciken manema labarai na jaridar The Punch ya gano cewa, wasu manyan ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya na bayar da guraben aiki ga wasu shafaffu da mai cikin sanatocin kasar nan.

Sai dai an tattaro cewa, kusoshin majalisar dattawan da ba su wuce mutum goma ba na kasafta guraben aikin a tsakaninsu ba tare da tsakuranwa sauran mambobin majalisar ba.

Wata majiya mai tushe a majalisar, ta ce bayyana karara yadda shugabannin majalisar suka kasafta guraben aiki guda 100 wanda hukumar tattara haraji ta kasar FIRS ta bai wa majalisar dattawan.

Fusataccen Sanatan da ya bukaci a sakaya sunansa wanda ya fito daga yakin Kudu maso Yamma, ya ce hukumar tattara harajin Najeriya, FIRS, ta bai wa majalisar dattawa guraben aiki 100 amma shugabannin majalisar sun kasafta su a tsakanin su.

Haka kuma Sanatan ya ce, su na da masaniyar yadda wani jigo cikin sanatocin Arewa maso Yamma ya rarraba wa al'ummar mazabarsa ta yankin Arewa maso Yamma guraben aiki 26, lamarin da ya ce hakan babbar matsala ce domin kuwa an yi tanadin aikin ne ga dukkanin al'ummar Najeriya ba wasu 'yan tsiraru ba.

"Hakan ya na nufin kenan sai ka san wani Sanata a kasar nan zaka samu aiki? Babu abinda ake yi kenan bisa ga cacanta."

"Matsalar wannan lamari shi ne ana daukar mutane dama aiki ba tare da an tantance su ba".

"Haka siddan an bai wasu shafaffu da mai guda 26 takardun daukan aiki na hukumar tattara haraji ta hanyar wani sanatan mazabar Arewa ta yamma yayin da sauran yankunan kasar kuma suka tashi fankanfayau."

KARANTA KUMA: Messi, Ronaldo da sauran 'yan kwallo 9 da suka fi kwazo a shekaru 10 da suka gabata

Sai dai wani sanatan da ya fito daga yankin Kudu maso Gabas, wanda shi ma ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa a bisa ka'ida ya kamata a bayar da gurbin aiki daya-daya ga kowane dan majalisar tarayya.

Da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Talata, shugaban kwamitin tabbatar da da'a na majalisar dattawa, Sanata Danjuma La'ah, yayin bayyana ci gaba bincike da kwamitinsa ya fara gudanar wa a makon da ya gabata, an gano yadda wasu manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya ke daukar aiki cikin sirri ba tare da tallata neman aikin ga al'ummar kasar ba.

Ire-iren ma'aikatun da Sanata La'ah ya wassafa sunayen sun hadar da hukumar tattara haraji, FIRS, hukumar yaki da ta'ammali da miyagn kwayoyi, NDLEA, Hukumar bincike ta sararin samaniya NASRDA, Jami'ar karatu daga-gida NOUN da kuma hukumar ayyukan gwamnatin tarayya.

anarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel