Kasafin Kudin 2020: Majalisar Dattawa ta dakatar da zamanta zuwa ranar 29 ga watan Oktoba

Kasafin Kudin 2020: Majalisar Dattawa ta dakatar da zamanta zuwa ranar 29 ga watan Oktoba

A ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2019, majalisar dattawan Najeriya, ta dakatar da zamanta har na tsawon makonni biyu domin bai wa ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin kasar nan damar kare kasafin kudin da suke sa ran batar wa a badi.

Shugaban majalisar, Sanata Ahmed Lawan, shi ne ya sanar da dage zaman majalisar a ranar Talata kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sanata Lawan ya ce majalisar ta zartar da hukuncin dakatar da zamanta domin samun damar tuntubar ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin kasar a kan kare kasafin kudin su na 2020.

Tun bayan gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa a ranar 8 ga watan Oktoba, Sanata Lawan ya bayar da umurni ga kowace ma'aikata ko hukumar gwamnati ta je gaban majalisar domin kare kasafin kudinta.

A cewar shugaban majalisar, za a dauki tsawon makonni biyu gabanin kowane ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati su kare kasafin kudinsu.

KARANTA KUMA: Boko Haram sun kashe sojoji 874 a Borno - Ndume

Shugaban Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudin Najeriya wanda ya wuce naira tiriliyan 10, ga zauren majalisar dokokin kasar a ranar Talata.

A Talatar makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudin Najeriya wanda ya wuce naira tiriliyan 10, a zauren majalisar dokokin tarayyar kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel