Boko Haram sun kashe sojoji 847 a Borno - Ndume

Boko Haram sun kashe sojoji 847 a Borno - Ndume

Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan sojin kasan Najeriya, Sanata Ali Ndume, ya ce kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, ta salwantar da rayukan dakarun soji 847 daga shekarar 2013 kawo wa yanzu.

Jaridar The Nation ta ambato Sanatan yana cewa, an binne gawarwakin sojojin da suka riga mu gidan gaskiya a wata makabartar dakarun soji da ke birnin Maidugurin jihar Borno.

Sai dai Sanatan ya ce wannan adadi bai hadar da na sojojin da mayakan Boko Haram suka hallaka ba kuma aka binne su a wasu makarbartun dakarun sojin na daban.

Furucin Sanata Ndume ya zo ne a yayin da mambobin kwamitin da yake jagoranta suka ziyarci jihar Borno.

Nduma ya ce binciken da kwamitinsa ya gudanar ya gano cewa sojoji da ke filin daga wajen tunkarar mayakan Boko Haram ba su da wadatattun kayan yaki kuma wadanda suka mallaka suna da nakasun nagarta.

KARANTA KUMA: A cikin shekaru hudu gwamnatin Buhari ta samu N16.6trn daga albarkatun man fetur

Hakazalika Sanatan ya ce adadin sojojin da ke tunkarar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin ya yi karancin gaske, lamarin da ya ke kiran gwamnatin Najeriya a kan aike wa da wasu dakarun domin an ce hannu da yawa maganin kazamar miya.

Ya kara da cewa, kwamitinsa na ci gaba a gudanar da bincike kan zargin wasu kungiyoyi masu zaman kansu da taimako da kuma goyon bayan mayakan Boko Haram.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel