A cikin shekaru hudu gwamnatin Buhari ta samu N16.6trn daga albarkatun man fetur

A cikin shekaru hudu gwamnatin Buhari ta samu N16.6trn daga albarkatun man fetur

A kididdigar wasu alkalumma na babban bankin Najeriya CBN, an gano adadi kudade da albarkarun man fetur suka tara wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wa'adinta na farko.

Alkalumman CBN sun tabbatar da cewa, daga watan Mayun 2015 zuwa Afrilun 2019, gwamnatin shugaban kasa Buhari ta samu Naira Tiriliyan 16.647 ta hanyar sayar da albarkatun man fetur.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, samun da gwamnatin Najeriya ta yi a zangon gwamnatin Buhari na farko bai hadar da samun sauran kamfanonin man fetur na 'yan kasuwa da ke kasar da masu zaman kansu.

An tattaro cewa, wannan tulin kudi da kasar Najeriya ta samu bayan fidda duk wasu nauye-nauye da hakkoki da ke kanta, ta kuma kasafta kudin a tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi.

KARANTA KUMA: Sojoji sun sake ceto wasu dalibai 4 da aka dauke a Kaduna

Bincike ya nuna cewa, arzikin da gwamnatin Buhari ta samu a shekaru hudu na zangon farko ta hanyar albarkatun man fetur ya yi kasa da kaso 43.6 cikin 100 na Naira Tiriliyan 29.514 da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta samu daga watan Mayun 2011 zuwa Afrilun 2015.

Dalla Dalla ga dai yadda adadin kudin shigar da gwamnatin Buhari ta samu daga albarkartun man fetur daga shekarar 2015 kawowa yanzu:

2015 - Naira Tiriliyan 2.3

2016 - Naira Tiriliyan 2.639

2017 - Naira Tiriliyan 4.109

2018 - Naira Tiriliyan5.63

Janairu zuwa Afrilun 2019 - Naira Tiriliyan 1.882.

Ga kuma yadda samun gwamnatin tsohon shugaban Jonathan ya kasance;

2011 - Naira Tiriliyan 8.094

2012 - Naira Tiriliyan 6.793

2013 - Naira Tiriliyan 6.809

2014 - Naira Tiriliyan 6.793

Janairu zuwa Afrilun 2015 - Naira Tiriliyan 1.497.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel