Sojoji sun ceto ragowar dalibai 4 da aka sace a Kaduna

Sojoji sun ceto ragowar dalibai 4 da aka sace a Kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar ceto ragowar dalibai hudu na wata makarantar sakandire a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa makaranta a ranar 10 ga watan Oktoba.

Mataimakin kakakin bataliyyar sojin Najeriya reshen jihar Kaduna, Kanal Ezindu Idiman, shi ne ya labarta wa manema labarai rahoton hakan a daren ranar Litinin da ta gabata yayin mika daliban cikin farin ciki ga iyayensu a kauyen Gurmi.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito, ana iya tuna cewa, a ranar 10 ga watan Oktoban da ta gabata ne masu garkuwa da mutane suka yi awon-gaba da dalibai 10 a kan hanyarsu ta zuwa makaranta.

A yayin da a koda yaushe take cikin jiran tsammani da ko ta kwana, jaridar Daily Trust ta ambato rundunar sojin tana cewa ta samu nasarar ceto dalibai guda shida daga cikin goman da masu garkuwa suka sace a safiyar Alhamis.

Haka kuma da misalin karfe 6.00 na safiyar Litinin, 14 ga watan Oktoba, rundunar sojin ta sake maimaita makamanciyar nasarar da ta samu inda ta ceto ragowar daliban hudu daga hannun masu garkuwa bayan ta yi wa maboyarsu kwanton bauna.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya 173 sun dawo daga kasar Libya

A wani rahoto mai nasaba da wannan, a jihar Kaduna da ke Najeriya, iyalai da kuma mazauna yankin Kajuru sun tabbatar da wani hari da 'yan bindiga suka kai, tare da yin awon-gaba da shugaban wata kwalejin ilimin kere-kere da ke yankin.

Mai dakinsa Amina ta bayyana wa BBC cewa 'yan bindigar sun tafi da shugaban makarantar ne mai suna Francis Mazi, bayan sun lakada masa dukan tsiya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel