Mafi karancin albashi: Gobe za'ayi zaman karshe tsakanin gwamnati da yan kwadago

Mafi karancin albashi: Gobe za'ayi zaman karshe tsakanin gwamnati da yan kwadago

Gwamnatin tarayya da yan kungiyar kwadago suna cikin tattaunawan karshe domin kawar da yiwuwan yajin aikin da ma'aikatakn Najeriya suka shirya ranar 16 ga watan Oktoba, 2019.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa yan kwadago sun yanke shawarar tafiya yajin aiki sakamakon rashin rashin cimma matsaya da gwamnati kan mafi karancin albashin N30,000.

Bangarorin biyu sun dade suna ganawa amma har yanzu ganawar bai haifi da mai ido ba.

Shugaban kwamitin kuma ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyana ranar Litinin cewa yana ganawa da bangarorin guda biyu domin kawar da yiwuwan yajin aikin da aka sanya ranar 15 ga Oktoba, saboda aka, gobe za'a yi ganawar karshe.

Ya yi kira ga shugabannin kungiyar kwadago su fadi ra'ayinsu a ganawar saboda a samu mafita daga cikin rikici na mafi karancin albashi.

A ranar Alhamis da ya gabata, Chris Ngige, ya bayyana cewa bukatar kungiyoyin kwadago na aiwatar da karin kudin mafi karancin albashi zai karawa gwamnatin tarayya nauyin N580 billion a kowani shekara.

Ngige ya ce wannan bukata da shugabannin kwadago keyi bai zai yiwu ba sai dai idan gwamnati za ta rage yawan ma'aikata domin cimma abinda suke so.

Ministan ya ce gwamnatin ba zata iya biyan kudin ba yanzu saboda babbar manufar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari shine inganta albashin kananan ma'aikatan gwamnati daga daraja ta 1 zuwa 6.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel