Fadar shugaban kasa ta caccaki ‘yar Mamman Daura akan fallasa bidiyon Aisha Buhari

Fadar shugaban kasa ta caccaki ‘yar Mamman Daura akan fallasa bidiyon Aisha Buhari

Wata majiya a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, ta ga laifin diyar Mamman Daura mai suna Fatima akan fallasa faifan bidiyon Uwargidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari.

Bidiyon da aka yada yayin da ake yada jita-jitan cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kara mata ta biyu a ranar Juma’a da ya gabata ya nuna sashin da uwar gidan Shugaban kasar, Aisha ke daga murya akan bukatar yan Gidan Mamman Daura su fita daga villa.

Wata majiya wacce ta ki bayyana sunanta ta bayyana cewa an dauki faifan bidiyon ne fiye da shekara daya da ya gabata, a lokacin da dan shugaban kasa, Yusuf yayi hatsari da babur dinsa a Abuja.

A cewarta, an bukaci yin amfani da wannan ginin wajen jinyar Yusuf. Tace umurnin cewa iyalan Daura su bar wajen ya fito ne daga shugaban kasar.

Majiyar ta kara da cewa duk da wannan umurni iyalan Daura sun ki bayar da hadin kai. Amma Fatima bata fadi hakan ba a hirarta.

KU KARANTA KUMA: Dan marigayi tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya mutu

Tace tabbass akwai wani makirci da aka kulla shiyasa aka saki bidiyon a yanzu, sannan cewa Fatima bata nuna bangarenta ba a bidiyo, inda suke rufewa uwargidar shugaban kasar kofa na wani yanki a fadar. Sannan kum,a cewa bata nuna muzancin da ta yiwa Aisha ba kafin ta mayar da martani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel