Ta'addanci: Sultan ya dau zafi, ya umurci gwamnoni da su tsige duk sarkin da aka samu da laifi sannan a jefa shi gidan yari

Ta'addanci: Sultan ya dau zafi, ya umurci gwamnoni da su tsige duk sarkin da aka samu da laifi sannan a jefa shi gidan yari

Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya yi kira ga gwamnoni da su tsige sannan kuma su gurfanar da duk wani basarake da aka samu da laifin goyon bayan rashin tsaro a masarautarsa.

Sultan ya nuna bacin rai game da zarge-zarge kan yanda wasu sarakuna suka tsunduma cikin harkar fashi da makami.

Sarkin Musulmin ya bada shawaran ne a ranar Litinin, 14 ga wata Oktoba, a wani babban taron kwana daya da aka gudanar akan lamarin tsaro a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara wanda majalisar sultan da kungiyar jaridun Najeriya suka hada kai suka kaddamar a majalisar jihar Sokoto.

Har ila yau ya bayar da shawarar cewa a samar da hukunci makamancin haka ga shuwagabannin addinai da aka samu suna goyon bayan rashin tsaro.

Daga karshe Sultan ya gwamnoni tabbacin samun goyon bayansa akan kokarin da ake na kawo karshen ayyukan ta'addaci a yankunansu.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Yanzun nan yan bindiga sun kai hari wata makaranta, sun yi garkuwa da yan gida daya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, yace ana gudanar da bincike sarakuna biyar da hakimai 33, bisa zarginsu da hannu a fashi da makami.

A wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, gwamnan yace yan sanda hudu da sojoji 10 ma na karkashin bincike akan wannan dalili guda. Yace duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel