Sarkin Kano ya sallameni don na karrama Ganduje - Maji Siddin Sarki

Sarkin Kano ya sallameni don na karrama Ganduje - Maji Siddin Sarki

Siddin Sarkin Kano, Alhaji Auwalu Maja, ya bayyana abinda ya faru mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya kwance masa rawani.

Ya bayyanawa manema labarai ranar Litinin a Kano cewa an sallameshi ne saboda ya karrama gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayinda da ya dawo daga Abuja bayan nasara a kotu.

Siddin Sarkin Kano, Alhaji Auwalu Maja, ya ce tun lokacin da sarki Sanusi ya hau mulki, an rage masa matsayi kuma ba'a bashi girman da ya cancanta.

Yace: "Lokacin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dawo Kano bayan makonni biyu da ya raka shugaba Muhammadu Buhari, ina daya daga cikin tarin jama'an da suka tarbesa."

"A ranar, na mika wani kayan sarki da hoton marigayi sarkin Kano, Ado Abdullahi Bayero ga gwamna Ganduje domin nuna masa farin cikina kan nasarar da ya samu a kotun zabe."

"Wannan abu daya da nayi ya sa sarkin Kano mai ci, Muhammad Sanusi, ya bada umurnin cewa a koresni daga gidan da nike zaune tsawon shekaru 20 yanzu."

"Bayan haka, an bukaci na mayar mukullan ofishina da dukkan dukiyan fada dake hannu na kuma na bi umurni."

"A yanayin aikina, ina aiki da Shamaki, Alhaji Wada Najalo, shine wanda ya wanzar da umurnin sarki na korata daga fada."

"Ba ni da wani kiyayya ga Sarki Sanusi ko wani a fada. Sun ci mutuncina kawai saboda na karrama gwamna Ganduje. Yanzu bukatana shine a mayar dani matsayina."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel