Siyasar Atiku Abubakar ba ta da wani karfi a Jihar Adamawa – Adamu Song

Siyasar Atiku Abubakar ba ta da wani karfi a Jihar Adamawa – Adamu Song

Mun ji labari cewa tsohon shugaban jam’iyyar adawa ta AD a Najeriya, Alhaji Adamu Song, ya fito ya yi fashin baki a game da siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

A wata hira da Daily Sun, Adamu Song yace ‘dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP a 2019 bai da karbuwa a gidansa jihar Adamawa duk da cewa siyasarsa ta yi karfi a fadin Najeriya.

A game da harkar siyasar jihar Adamawa, Song ya bayyana cewa mutanen jihar wayayyun gaske ne don haka babu wanda ke yi masu katsalandan daga waje saboda yanayin Mazaunan yankin.

Dattijon na Arewa ya na da ra’ayin cewa mutanen jihar Adamawa su na cikin wadanda su ka fi kowa wayewa inda ya dogara da yadda ake zaman lafiya a jihar duk da banbancin addininsu.

KU KARANTA: Kasa ta goyi bayan Buhari a kan rufe kan iyakokin Najeriya

Tsohon shugaban jam’iyyar adawar na kasa yake cewa masu tunanin Atiku ya na da wani karfi a Adamawa sun yi kuskure domin duk da Atiku ya na da karfi a kasa, bai da ta cewa a jihar.

A cewar tsohon Sakataren na NUPENG, babu wanda zai kashewa tafiyar Atiku Abubakar sisin kobo ba tare da ya aika masa takardar abin da ya kashen domin a biyasa duk kudin na sa ba.

‘Dan siyasar wanda ya ga jiya ya gau yau, ya kuma tafo albarkacin bakinsa game da yadda zaben 2023 zai iya kasancewa inda ya bayyana cewa zai yi wahala mutanen Arewa su zabi Inyamuri.

Song bai dai bayyana wanda ya ke ganin zai iya samun nasara a zabe mai zuwa ba amma ya nuna shakkunsa game da sabon kiran da ake yi na ganin cewa mulki ya koma hannun mutanen Ibo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel