Babu wanda ya kaiwa Oshiomhole hari – Kwamishinan yan sandan Edo

Babu wanda ya kaiwa Oshiomhole hari – Kwamishinan yan sandan Edo

Kwamishinan yan sandan jihar Edo, DanMallam Muhammed ya sake jaddada matsayar rundunar yan sandan reshen cewa babu harin da aka kai gidan tsohon gwamnan jihar kuma Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Comrade Adams Oshiomhole.

Muhammed wanda ya fadi haka a hira da manema labarai a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, ya yi watsi da zarge-zargen hari akan tsohon gwamnan, inda ya gargadi masu rura wutar rikici da su rabu da jihar.

Kwamishinan yan sandan yace yan sandan sun karfafa matakan tsaro kewaye da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa yayin da ya kai ziyara jihar, a lokacin kuma babu harin da aka kai masa.

Wani jigon APC a jihar, Charles Idahosa ya bayyana zarge-zargen a matsayin wani yunkuri da bata gari ke yi don hargitsa lamarin siyasa ta yanda miyagun mutane zasu iya samun damar daukaka mugun aniyyarsu.

KU KARANTA KUMA: Matsalar tsaro: Sarakuna 5, hakimai 33 da sojoji 10 na karkashin bincike – Gwamna Matawalle

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto a baya cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshiomhole ya na fuskantar kalubale bayan gwamnonin jam’iyyar sun shiga cikin masu taso sa.

Jaridar tace idan aka tafi a haka, kwanakin Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya na kasa su na daf da zuwa karshe har an fara tunanin zai iya rasa mukaminsa a farkon shekarar 2020.

Hakan na zuwa ne bayan da aka fara jin kishin-kishin cewa wasu daga cikin gwamnonin APC sun bi zugar da ke neman ganin bayan shugaban jam’iyyar. Yanzu dai Oshiomhole ya na kan siradi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel