Kasafin kudi: Sojojin Najeriya sun warewa harkar abinci Miliyan 84

Kasafin kudi: Sojojin Najeriya sun warewa harkar abinci Miliyan 84

Ma’aikatar tsaro a Najeriya ta ware makudan kudi har sama da Naira miliyan 70 wajen jin dadi da walwalan dakaru da ma’aikatanta kamar yadda kasafin kudin shekara mai zuwa na nuna.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sojojin za su kashe N71, 071, 578 a kan harkar jin dadin jami’ai, sannan kuma za a batar da wasu N13, 436, 544 wajen sayen kayan abinci a shekarar badin.

Jimilar abin da ma’aikatar tsaron za ta batar a kan sayen makamai a kasafin kudin shekarar 2020 shi ne Naira miliyan 80. A halin yanzu dai ana fuskantar rashin tsaro a bangarorin kasar nan.

Wani binciken kurilla da aka yi wa kasafin kudin Najeriya ya sa an gane cewa ma’aikatar tsaron ta yi kasafin Naira miliyan 89 wajen zirga-zirga cikin Najeriya da kuma yawo a fadin Duniya.

KU KARANTA: Jiragen fadar Shugaban kasa za su lashe miliyan 700 a kasafin kudin 2020

Har ila yau, abin da aka ware za a batar domin bincike da cigaba a bangaren tsaron kasar Naira miliyan 16 ne rak. Hakan na nufin kudin zirga-zirga da cin abinci ya zarce na aiki da bincike.

Daga cikin manyan ayyukan da ma’aikatar tsaron ta tsara za ta yi a badi akwai sayen motoci na Naira miliyan 46. Bayan nan kuma za a kashe N1, 800, 000, 000 wajen gyaran barikin Sojoji.

Ma’aikatar ta sa aikin gyare barikin Sojojin kasar nan da ke fadin bangarorin Najeriya shida a matsayin manyan shirin da ta ke da su a shekara mai zuwa domin gyara wurin zaman jami’an.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel