Matsalar tsaro: Sarakuna 5, hakimai 33 da sojoji 10 na karkashin bincike – Gwamna Matawalle

Matsalar tsaro: Sarakuna 5, hakimai 33 da sojoji 10 na karkashin bincike – Gwamna Matawalle

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, yace ana gudanar da bincike sarakuna biyar da hakimai 33, bisa zarginsu da hannu a fashi da makami.

A wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, gwamnan yace yan sanda hudu da sojoji 10 ma na karkashin bincike akan wannan dalili guda.

Yace duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

“Sarakuna biyar, hakimai 33, yan sanda hudu da sojoji 10 na karkashin bincike kamar yadda muke ganin suna da hannu a abubuwan dake gudana a jihar. Idan aka same su da laifi wajen taya da assasa fashi da makami, zasu fuskancci hukunci daidaida doka. Babu wani hukunci da ya cika tsanani,” ya wallafa a shafin twitter.

A baya mun ji cewa wani kwamitin gudanar da bincike a kan matsalar tsaro da jihar Zamfara ke ci gaba da fuskanta wanda gwamna Muhammadu Bello Matawalle ya kafa, ya gano wadanda ke da hannu kan haifar da wannan mummunar annoba a jihar.

Kwamitin ya gano cewa wasu bata garin jami'an tsaro na soji da kuma na 'yan sanda gami da sarakunan gargajiya na da hannu wajen assasa matsalar rashin tsaro a jihar.

Yayin mika rahoton a ranar Juma'ar da ta gabata, jagoran kwamitin binciken wanda ya kasance tsohon sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Alhaji M.D Abubakar, ya ce an gano cewa wasu sarakuna 5, dagatai da masu unguwanni fiye da 40 masu hannu cikin badakalar rashin tsaro a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel