Abinda yasa karin albashi ba zai taimaki ma'aikatan Najeriya ba - Ahmed Makarfi

Abinda yasa karin albashi ba zai taimaki ma'aikatan Najeriya ba - Ahmed Makarfi

- Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya ce neman karin albashi da ma'aikta ke yi ba shine abu mafi muhimmanci ba

- Tsohon gwamnan ya bukaci ma'aikatan gwamnati su mayar da hankali wajen tilasta gwamnati yin aiki bisa gaskiya da adalci

- Kazalika, ya bayyana cewa samar da abubuwan more rayuwa zasu rage yawan kudin da ma'aikata ke kashe wa a wata

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya yi gargadi a kan bawa kudi fifiko a cikin tsarin aikin gwamnati a Najeriya.

Makarfi, tsohon sanatan Najeriya daga jihar Kaduna, ya fadi hakan ne yayin taron tsofin daliban makarantar hadaka ta tarayya (USOSA) da ke garin Kaduna.

Tsohon gwamnan, wanda mamba ne a kungiyar USOSA, ya ce kamata ya yi ma'aikata su bukaci shugabanni su gudanar da jagorancin gwamnati bisa gaskiya da rikon amana sabanin neman koda yaushe a kara musu kudi.

Makarfi ya bukaci ma'aikatan gwamnati su mayar da hankali wajen tilasta gwamnati yin aiki bisa gaskiya da tsarin doka.

DUBA WANNAN: Wutar lantarki: Jonathan da Buhari sun kashe tiriliyan N1.164 a cikin shekaru 8

"Kudi ba zasu yi wa ma'aikata wani amfani ba, na san da wanna kalubalen tun kafin na zama gwamna, kuma su ma shugabannin kungiyar kwadago sun san da hakan.

"Sabanin neman karin kudi kowanne lokaci, kamata ya yi ma'aikata su bukaci shugabanni su gudanar da jagoranci bisa adalci, su nemi a inganta tsaro, a samar da abubuwan more rayuwa, su nemi abubuwa daga wurin hukuma da zasu saukaka musu rayuwa da yawan kashe kudi.

"Amma idan kullum kudi ka ke bukata, sai wani ya baka N10 amma ya dauke maka N30, da me ka karu kenan?", a kalaman tsohon gwamna Makarfi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel