EFCC ta kai mamaya wani gidan rawa, ta kama mutane 94 da manyan motoci 19

EFCC ta kai mamaya wani gidan rawa, ta kama mutane 94 da manyan motoci 19

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen jihar Ibadan a ranar Litinin sun kai mamaya wani gidan rawa a Osogbo, kulob din da ya shahara wajen shirya wa yan damfara ta yanar gizo nishadi.

Wannan samame da jami'an suka kai gidan rawan yayi sanadiyyar kama masu laifi 94 da kuma kwato manyan motoci masu tsada guda 19, na'urar lafto, wayoyi da sauran kayayyaki.

Shahararren gidan rawan mai suna ‘Club Secret Underground’ ya kasance a hanyar babban titin Ibadan-Iwo a babban birni Jihar.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren a wani jawabi da ya gabatar ya bayyana cewa hukumar ta daukaka aikin ne bayan bayanan kwararru da ta samu cewa yan damfara suna taron nishadi da murnar nasara da suka samu a wajen damfaran mutane.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago sun sa labule kan aiwatar da N30,000 karacin albashi

Uwujaren yace masu laifin a halin yanzu suna cigaba da fuskantan bincike, inda ya kara da cewa za’ a gurfanar da wadanda ke da hannu cikin lamarin a kotu bayan an kammala bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel