Gwamnatin Neja ta rufe makarantu guda 2000 marasa inganci a Suleja

Gwamnatin Neja ta rufe makarantu guda 2000 marasa inganci a Suleja

Gwamnatin jahar Neja ta sanar da rufe akalla makarantu masu zaman kansu guda 2000 sakamakon rashin ingancinsu, musamman a karamar hukumar Suleja da sauran yankunan jahar, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban sakataren ma’aikatar ilimi na jahar Neja, Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin wata ganawa da yayi da shuwagabannin kungiyoyin yan kasuwa masu makarantun kudi, NAPPS.

KU KARANTA: Ma’aikatan kananan hukumomi sun jinjina ma El-Rufai game da samun karin albashi

Yayan kungiyar NAPPS sun kai ziyara fadar gwamnatin jahar ne domin murnar zagayowar ranar kungiyar NAPPS ta duniya, a yayin ganawar tasu ne Aliyu ya bayyana cewa sun rufe makarantun ne saboda rashin inganci.

“Muna da kwamitin sa ido dake zagayawa makarantun kudi dake babban birnin jahar da kananan hukumomi domin tabbatar da ingancin makarantu, tare da tabbatar da suna aiki kamar yadda gwamnati ta tsara musu.

“Amma a makarantu da dama mun tarar da basu da bayi, ofisoshi, ruwan amfani, dakunan karatu, kai wasu ma basu da isassun malamai da zasu koyar da daliban. Wannan na daga cikin aikinmu na tabbatar da ingancin ilimi a jahar nan.”

Sa’annan ya baiwa kungiyar NAPPS tabbacin gwamnati za ta duba matsalar yawan karba haraji daban daban daga makarantun tare da magacenta.

Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban NAPPS, Dakta Sally Bolujoku ya bayyana cewa suna murnar zagayowar ranar ne domin duba matsalolin da ke da akwai a sha’annin ilimi tare da shawo kansu gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel