Ma’aikatan kananan hukumomi sun jinjina ma El-Rufai game da samun karin albashi

Ma’aikatan kananan hukumomi sun jinjina ma El-Rufai game da samun karin albashi

Tun bayan kaddamar da karin albashin da gwamnatin jahar Kaduna a karkashin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ta yi ma ma’aikatun gwamnatin jahar, jama’a da dama suke bayyana farin cikinsu tare da jinjina ma gwamnatin.

A nan ma ma’aikatun karamar hukumar Sanga da na Kaura ne suka bayyana farin cikinsu game da samun wannan karin, tare da bayyana godiyarsu ga shuwagabannin kananan hukumomin bisa zartar da wannan karin albashi.

KU KARANTA: Rundunar Sojin sama ta zazzaga ma yan ta’adda ruwan bamabamai a Borno

Ma’aikatan sun bayyana haka ne a kungiyance a karkashin jagorancin kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi cikin wasu tattaunawa da suka yi da kamfanin dillancin labaru ta Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikatan suna yabawa game da matakin karin albashin, inda suka ce yadda kananan hukumomi suka kara albashi tun kafin ma gwamnatin tarayya ta kara ya nuna sun damu da halin da jama’ansu suke ciki, tare da baiwa walwalarsu fifiko.

Shugaban kungiyar NULGE reshen karamar hukumar Sanga, John Mazo ya bayyana cewa: “Babu shakka wannan mataki zai kara ma ma’aikata kwarin gwiwa musamman wajen kara kwazo a ayyukan da suke gudanarwa.

“Yayin da muke jinjin ma shugaban karamar hukumar Sanga, Charles Danladi bisa kokarin da ya yi, muna kira ga ma’aikata dasu jajirce wajen tabbatar an cimma manufofin karamar hukumar, domin kuwa yaba kyauta tukwuici.” Inji shi.

Shima a nasa jawabin, shugaban NULGE reshen karamar hukumar Kaura, Philip Joseph ya nanata irin kiran da John Mazo ya yi, sai dai yace shugaban karamar hukumar Kaura, Bege Ayuba ya zama gwarzo abin koyi ta hanyar kara ma ma’aikata albashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel