Gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago sun sa labule kan aiwatar da N30,000 karacin albashi

Gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago sun sa labule kan aiwatar da N30,000 karacin albashi

Wakilan gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, sun gana da shugabannin kungiyar kwadago kan aiwatar da sabon karancin albashi na N30,000 da kuma yin gyara a albashin ma’aikatan gwamnati.

An fara ganawar ne jim kadan bayan isowar mambobin kungiyar a ma’aikatar kwadago da daukar ma’aikata a Abuja, babbar birnin tarayya.

A jawabinsa, ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr Chris Ngige, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana shi a matsayin koro jawabi wanda ke kwaranya daga taron baya tsakanin gwamnati da shugabannin kwadago.

Ministan ya ba shugabannin kungiyar tabbacin cewa zai cigaba da kasancewa a tsaka-tsaki a dukkanin tattaunawar.

Sannan kuma ya yaba ma mambobin kungiyar akan nuna wasu fahimta da suka yi.

Ngige ya sanar da cewa za a sake wani zama tare da shugabannin hukumomin gwamnati, inda za a bude litattafansu domin ganin nawa za a iya biyan ma’aikata.

KU KARANTA KUMA: Wannan tsarin da Buhari ke bi shine ke haifar da rashawa - Clarke

A cewarsa za a yi ganawar a ranar Talata.

Da fari an hana yan jarida daukar rahoton ganawar wanda aka yi cikin sirri amma daga bisani sai ministan ya basu damar shiga.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel