Wutar lantarki: Jonathan da Buhari sun kashe tiriliyan N1.164 a cikin shekaru 8

Wutar lantarki: Jonathan da Buhari sun kashe tiriliyan N1.164 a cikin shekaru 8

Duk da mafi yawan sassan Najeriya basa samun hasken wutar lantarki, gwamnatin tarayya ta kashe fiye da tiriliyan N4.7 a bangaren wutar lantarki daga shekarar 1999 zuwa 2010.

Shekaru takwas bayan hakan, gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da gwamnati mai ci ta shugaba Buhari, sun kara kashe karin tiriliyan N1.164 a bangaren wutar lantarki, amma har yanzu masana'antun cikin gida sun dogara ne da injina domin samun wutar lantarki.

Beatrice Ogbor, wata yarinya mai shekaru shidda, da dan uwanta mai shekaru biyu a duniya, basu taba ganin hasken wutar lantarki ba a yankinsu, basu ma san ana yin ihun 'NEPA' ba idan an kawo wuta a Najeriya ba.

"Mun haife ta a shekarar 2014, amma zaku yi mamaki idan na fada muku cewa ita da dan uwanta basu taba ganin hasken wutar lantarki ba tunda aka haife su," a cewar John Ogbor, mahaifin yaran.

DUBA WANNAN: Zaben Nuwamba: Tsohon mataimakin gwamna da jiga-jigan 'ya'yan PDP sun fice daga jam'iyyar a Bayelsa

Ogbor, dan asalin garin Igede da ke karamar hukumar Obi a jihar Benuwe, yana zaune ne tare da iyalinsa a unguwar Moro da ke karamar hukumar Shagamu a jihar Ogun.

Duk da ya shafe tsawon shekaru 14 yana zaune a Moro, Ogbor ya ce kusan shekaru 7 kenan rabon da su ga hasken wutar lantarki a unguwarsu.

Babban abin tambaya da damuwar shine; ina dukkan wadannan makudan kudi da ake ikirarin an kashe a bangaren samar da wutar lantarki suka shige?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel