Rundunar Sojin sama ta zazzaga ma yan ta’adda ruwan bamabamai a Borno

Rundunar Sojin sama ta zazzaga ma yan ta’adda ruwan bamabamai a Borno

Hukumar Sojin sama ta sanar da lalata wani sansani da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ke amfani da shi wajen gudanar da tarukanta a cikin yankin Boboshe dake gefen dajin Sambisa a jahar Borno.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kaakakin hukumar Sojan sama, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Tsige Maja Sirdin Sarki ta janyo cece kuce da nuna ma juna yatsa a fadar Sarkin Kano

A jawabinsa, Ibikunle ya bayyana cewa dakarun Operation Lafiya Dole ne suka kaddamar da harin a ranar Lahadi bayan samun bayanan sirri dake tabbatar da tattaruwar yan ta’addan na Boko Haram.

“Mun samu tabbacin rahoton dake nuna cewa akwai wani gida da yan ta’adda suke amfani dashi wajen gudanar da taruka, inda daga nan manyan kwamandojinsu suke basu jawabi kafin su kai ma Sojoji da jama’an gari hari.

“Da wannan rundunar ta aika jirgin yakinta zuwa sansanin, inda aka samu nasara ya zazzaga ruwan bamabamai a sansanin, wanda hakan yasa ya rugurguza sansanin gaba daya, tare da halaka yan ta’adda da dama” Inji shi.

Daga karshe rundunar ta yi alkawarin cigaba da aiki tukuru, tare da aiki kafad da kafada da Sojojin dake kasa domin kakkabe ragowar mayakan ta’addanci daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

A wani labarin kuma, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya bayyana cikin wani sabon bidiyo inda ya gargadi gwamnan jahar Borno, Bagana Umara Zulum sa’annan ya yi kira ga al’ummar Borno dasu tuba, su koma ga Allah ta hanyar shiga Musulunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel