Zaben gwamnan Kogi: APC ta ambaci sunan wanda zai iya kayar da Yahaya Bello

Zaben gwamnan Kogi: APC ta ambaci sunan wanda zai iya kayar da Yahaya Bello

Kungiyar kamfen din gwamnan jihar Kogi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tace tana da karfin gwiwar cewa Gwamna Yahaya Bello zai yi nasara a zaben jihar mai zuwa.

Kingsley Fanwo wanda ya kasance Shugaban labarai na kungiyar kamfen din ne ya bayyana hakan a Lokoja, jaridar The Nation ta ruwaito.

A cewar Fanwo, APC ta samu Karin goyon baya daga mutane jihar da manyan masu ruwa da tsaki wanda zai taimaka wa gwamnan wajen samun tazarce.

Ya bigi kirjin cewa Gwamna Bello ne kadai zai iya kayar da kansa a zaben mai zuwa, inda ya kara da cewa dawowar yan takarar da suka kara da gwamnan a lokacin zaben fidda gwamni ya kara bunkasa damar APC na yin nasara sosai.

Fanwo yayi ba a ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), cewa jam’iyyar ta rasa shugabanninta da dubban magoya bayanta a hannun APC.

KU KARANTA KUMA: Wannan tsarin da Buhari ke bi shine ke haifar da rashawa - Clarke

Ya kuma bayyana cewa PDP ta rasa sanata guda da take dashi, Dino Melaye, inda ya kara da cewa kwanan nan za a maye gurbinsa da Sanata Smart Adeyemi a majalisar dattawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel