Idan kuka siya mana jirage masu angulu, Boko Haram za ta zama tarihi - Hukumar Soji

Idan kuka siya mana jirage masu angulu, Boko Haram za ta zama tarihi - Hukumar Soji

Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi, ya bayyana cewa idan gwamnati ta hukumar soji kayayyakin yakin da suke bukata, cikin dan kankanin lokaci zasu karar da yan Boko Haram.

Babban jami'in Sojan ya bayyana cewa rashin jiragen yaki ne ya sa suka gaza kawar da yan ta'addan.

Ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dokokin tarayya a Maiduguri, jihar Borno ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2019.

Adeniyi ya ce yan Boko Haram ba wasu mayaka masu karfi bane kamar yadda ake tunani.

Yace: "Abinda hukumar Sojin Najeriya ke bukata kadai shine sashen jirgin sama na kanta kuma da jiragenta."

"Akwai hanyar magance wannan matsalan da za'a samu natija. Hukumar Soji na bukatar jirage masu saukar angulu domin kawo karshen yakin Boko Haram. Idan muna da shi, ba zamu yi amfani da shi kamar yadda hukumar sojin sama ke yi."

"Wadannan jiragen zasu kasance tare da mu a faggen yaki, zamu rika amfani da su tare da bindigoginmu."

"Na san an dade ana tattauna hakan. Idan aka yi, Najeriya za ta manta da Boko Haram."

"Bari in bayyana cewa yan Boko Haram ba wasu mayaka bane. basu da karfi, ba zasu iya kwashe mintuna 15 ana artabu ba. Ni da kaina nayi musayar wuta da Boko Haram a Marte, Delta da Gubio."

Asali: Legit.ng

Online view pixel