Rundunar sojin Najeriya za ta samu karin sojoji 4,832 a mako mai zuwa

Rundunar sojin Najeriya za ta samu karin sojoji 4,832 a mako mai zuwa

Rahotanni sun kawo cewa rundunar sojin Najeriya za ta kwashi karin sojoji 4,832 cikin dakarunta don karfafa ayyukanta a fadin kasar cikin mako mai zuwa.

Kwamandan rundunar sojin kasar, Manjo Janar Sani Mohammed ne ya bayyana haka a karshen makon da ya gabata, a lokacin bikin shigan sabbin jami’ai karo na 78; taron da ya kawo karshen horarwa daban daban da aka yiwa sabbin dauka.

A cewar shi, akan kaddamar da bikin ne don girmama sojojin da suka yi nasara yayin gudanar da hararwan, inda yake cewa za a kaddamar da sabbin dauka mutum 4,832 a ranar 19 ga watan Oktoba bayan gudanar da fareti.

A jawabin shi, Shugaban rundunan sojin Najeriya, Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai ya yabi kwamandan da leftanoninsa bisa shigo da sabbin daukan cikin tsarin.

KU KAANTA KUMA: Yar Mamman Daura ce ta dauki bidiyon Aisha Buhari tana fada

Tare da wakilcin manjo Janar Aminu Bichi Maitama (rtd), Buratai yace horarwa a rundunan sojin Najeriya tsaro ne dake daukan lokacin a rayuwar soja.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani kwamitin gudanar da bincike a kan matsalar tsaro da jihar Zamfara ke ci gaba da fuskanta wanda gwamna Muhammadu Bello Matawalle ya kafa, ya gano wadanda ke da hannu kan haifar da wannan mummunar annoba a jihar.

Kwamitin ya gano cewa wasu bata garin jami'an tsaro na soji da kuma na 'yan sanda gami da sarakunan gargajiya na da hannu wajen assasa matsalar rashin tsaro a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel