Sanusi ya karyata sallamar basarake saboda yiwa Ganduje maraba

Sanusi ya karyata sallamar basarake saboda yiwa Ganduje maraba

Masarautar Kano a ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoba, ta karyata labarin dake yawo na cewa ta kori Maja Siddin Sarkin Kano, Alhaji Auwalu, wanda ke da alhakkin kula da dokin sarki.

Zargin sallamar nasa na ta yawo a yanar gizo cewa a ranar Asabar Sanusi ya sallame shi sannan yayi umurnin Auwalu ya tattara ya bar gidasa da ke a cikin fadar a matsayin hukuncinsa na shiga gangamin masu yiwa Gwamna Abdullahi Ganduje maraba da dawowa a ranar Laraba da ya gabata.

Sai dai wata majiya a fadar sarkin ta bayyana cewa kawai dai masarautar ta karbi makulin garken masarautar ne daga hannun jigon, biyo bayan ganowa da tayi cewa wasu muhimman abubuwa sun bata a garken.

Maja Siddin ne ke kula da garken masarautar na tsawon lokacin.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya zabi kwamishinoni na jihar Kano

Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi ya karyata rahoton.

A halin da ake ciki, mun ji cewa tun bayan bayyana rahoton dake nuna cewa mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya tsige guda daga cikin bafadensa, watau Maja Sirdi, Alhaji Auwalu Idi, batun ya tayar da kura a fadar masarautar Kano.

Jaridar KanoFocus ta ruwaito maja sirdin ya tabbatar da tsigeshi a kan wannan laifi da Sarkin ke tuhumarsa da aikatawa, inda yace shamakin Kano, Wada Jalo ne ya umarci ya tashi daga gidan a da yawun Sarki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel