Fadar Shugaban kasa ta ja baya a rikicin Gwamnoni da Shugaban APC Oshiomhole

Fadar Shugaban kasa ta ja baya a rikicin Gwamnoni da Shugaban APC Oshiomhole

Rahotanni daga Jaridar Daily Sun su na nuna cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshiomhole ya na fuskantar kalubale bayan gwamnonin ja,’iyyar sun shiga cikin masu taso sa.

Jaridar tace idan aka tafi a haka, kwanakin Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya na kasa su na daf da zuwa karshe har an fara tunanin zai iya rasa mukaminsa a farkon shekarar 2020.

Hakan na zuwa ne bayan da aka fara jin kishin-kishin cewa wasu daga cikin gwamnonin APC sun bi zugar da ke neman ganin bayan shugaban jam’iyyar. Yanzu dai Oshiomhole ya na kan siradi.

Majiyar Jaridar ta Daily Sun tace abin da ya ke ceton Oshiomhole a wannan lokaci kurum shi ne sa bakin da fadar shugaban kasa ta yi a cikin rikicin. A wani bangare, an musanya wannan jita-jita.

“Fadar shugaban kasa ta shiga cikin maganar, ta na rokon duk masu jin haushin Oshiomhole su yi hakuri su ajiye kayan fadansu har zuwa lokacin da aka kammala shari’ar zaben shugaban kasa.”

KU KARANTA: Aisha Buhari ta duro Najeriya bayan wata da watanni a kasar waje

Majiyar ta kuma kara da: “Fadar shugaban kasar ta na ganin ba zai yi wa jam’iyya kyau ta samu sabani a daidai lokacin da ake jira kotu ta yanke hukunci a kan karar babban zaben 2019 ba.”

Gudun APC ta samu kan ta a rabe yayin da ake tsakiyar shari’a ne ya sa aka fasa yunkurin tsige Oshiomhole daga kujerarsa. Ganin cewa yanzu an tsallake shari’ar farko, an dawo da batun.

“Akwai tarin hujjojin sauke shi, kuma ina tabbatar maka cewa Oshiomhole ba zai kasance a kan kujerar shugaban APC na kasa zuwa bayan Watan Junairun shekara mai zuwa ba.” Inji Majiyar.

Rahotanni sun ce gwamnonin za su nemi a tsige Oshiomhole muddin ya ki bin hanyar lalama ya ajiye aikin da kansa. Sai dai Hadimin shugaban jam’yyar, Simon Ebegbulem ya karyata wannan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel