Kishin-kishin: Talabijin da gyare-gyaren jiragen shugaban kasa za su ci miliyan 700

Kishin-kishin: Talabijin da gyare-gyaren jiragen shugaban kasa za su ci miliyan 700

Rahotanni na yawo cewa gwamnatin tarayya ta yi kasafin Naira miliyan 792 a matsayin abin da za a kashe domin inganta talabijin da ke cikin wani babban jirgi da shugaban kasa ya ke hawa.

The Nation ta kuma bayyana cewa za a kashe kudi wajen kafa sababbin na’urorin kallon gidan talabijin kai-tsaye tare da samun damar hawa shafukan yanar gizo a cikin jirgin BBJ 5N-FGT.

A cewar Jaridar wadannan miliyoyi su na cikin abin da aka ware a kasafin kudin shekara mai zuwa. Bayan haka kuma za a batar da miliyan 50 wajen yin aiki a wani jirgin na G550 5N-FGW.

Rahoton da jaridar ta The Nation ta fitar ta ce gwamnatin tarayya ta na neman miliyan 650 domin gyara wani jirgin saman shugaban kasar. Za a kashe miliyan 20 ne a kan sayen wani igiyan jirgin.

KU KARANTA: Majalisar Liberiya ta na neman hanyar matse bakin aljihu a 2020

Bangaren wannan kudi, miliyan 90 za su tafi ne wajen sayen kayan kashe wuta saboda gudun bacin-rana. Za kuma a batar da miliyan 25 wajen sayen wasu kayan da ake bukata a cikin jirgin.

Daga cikin gyare-gyaren da za a yi, akwai na’urar da za a kafa mai amfani da kati domin gane mai shiga jirgin. Ana sa ran a yi wa wasu jiragen sababbin zubi wanda wadannan za su ci miliyan 45.

Har ila yau, a cikin kasafin kudin na Najeriya na 2020, hukumar tsaro na DSS za su kashe kusan miliyan 200 wajen sayen jiragen nan na zaman marasa matuki domin inganta tsaro a fadin kasar.

Wadannan jirage na fadar shugaban kasa sun dade su na lashe makudan miliyoyi. Wannan ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba yin alkawarin zai sa wasu daga cikinsu a kasuwa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel