Za a zaftare albashin ‘Yan Majalisa da Sanatocin Liberiya da kashi 31 da 36

Za a zaftare albashin ‘Yan Majalisa da Sanatocin Liberiya da kashi 31 da 36

‘Yan Majalisar Najeriya za su yi bindiga da Naira biliyan 125 a shekara mai zuwa. A daidai wannan lokaci ne kuma mu ke jin cewa ana neman rage albashin ‘Yan Majalisar a kasar Liberiya.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar 13 ga Watan Oktoba, ‘yan majalisar tarayyar Liberiya, sun amince da ragin albashin ne a lokacin da su ka soma aiki a kan kasafin kudin kasar na 2020.

Liberiya ta na sa ran batar da Dala miliyan 526 a shekara mai zuwa inda daga ciki ake neman hanyar daukar ma’aikatan lafiya 1200. Wannan ya sa ‘yan majalisar su ka amince su rage kudinsu.

A cewar wata Mujallar kasar ta FrontPageAfrica, ‘yan majalisar Wakilai da Sanatoci sun yi amfani ne da hasashen da hukumar IMF ta yi inda su ka gujewa aron kudi kamar yadda aka saba a baya.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya sa Shugaban Afrika ta Kudu ya fashe da dariya ana tsakiyar zama

Daga 2020, ‘Yan Majalisar wakilan kasar za su rasa 31% daga cikin abin da su ka saba karba duk wata. Abokan aikinsu watau Sanatoci kuma sun yi na’am da ragin 36% daga cikin albashin na su.

Bayan haka kuma kasar ta cire Dala miliyan 7 da ta saba warewa a cikin kasafinta domin in ta kwana. Wannan duk ya na cikin dabarun da gwamnati ta kawo na matse bakin aljihu a 2019/20.

Kasafin da gwamnatin tarayyar kasar Liberiya ta yi da farko ya haura Dala miliyan 530. Bayan kundin kasafin ya shigo hannun majalisa ne su ka rage abin da za a kashe zuwa fam miliyan 520.

Bayan rage kudin da ake warewa ‘yan majalisa, an kuma zaftare wani kaso daga cikin albashin Alkalan Liberiya. A Najeriya ‘yan majalisa 469 za su tashi ne da Biliyan 125 a shekarar badi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel