Har ila yau: Shekau ya sake sakin sabon bidiyo, ya aika sako ga gwamna Zulum

Har ila yau: Shekau ya sake sakin sabon bidiyo, ya aika sako ga gwamna Zulum

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sake fitar da sabon faifan bidiyo a ranar Lahadi domin yin martani ga kalaman gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a kan yin kira ga mayakan Boko Haram da su ajiye makamansu domin rungumar tsarin yafiya da gwamnatin jihar ta bullo da shi.

A cikin faifan bidiyon mai tsawon mintuna 18, Shekau ya yi magana a cikin harsunan Kanuri da Hausa, inda ya nuna kin amincewarsa da ikirarin gwamna Zulum a kan cewa wasu daga cikin mayakan Boko Haram an tilasta zama mambobin kungiyar ne kuma sun gaji da yakin da suke yi.

Shekau ya bayyana cewa babu wani mamba a cikin kungiyar Boko Haram da ya shiga bisa dole ko don tsoro tare da bayyana cewa basu gaji da yaki ba, zasu cigaba har sai sun daina numfashi.

Wannan shine bidiyo na farko da Shekau ya saki a cikin 'yan watannin baya bayan nan.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kwato wasu yara 8 da aka sayar a Anambra bayan an sace su a Kano

A cikin faifan bidiyon, Shekau ya kunna sautin muryar gwamna Zulum yayin da yake gabatar da jawabi ga taron jama'a. A cikin faifan sautin muryar, gwamnan ya yi kira ga mambobin kungiyar Boko Haram da su ajiye makamansu domin rungumar tsarin yafiya na gwamnati.

A cikin sautin muryar da Shekau ya kunna, gwamna Zulum ya rufe jawabinsa da ayar Qur'ani mai girma, wacce ke cewa 'Allah yana yafe zunubai'.

Sai dai, Shekau, wanda ya yi ikirarin cewa shi mahaddacin Qur'ani ne, ya ce gwamnan bai fahimci abinda ayar ke magana a kai ba, a saboda haka bai yi amfani da ita a wurin da ya dace ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel