2023: An bude ofishin yakin neman zaben Tinubu a jihar kudancin Najeriya

2023: An bude ofishin yakin neman zaben Tinubu a jihar kudancin Najeriya

Jitar-jitar da ake yada wa a gari a kan cewa jagoran jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, na son ya gaji kujerar shugaba Buhari a shekarar 2023 na neman zama gaskiya bayan wasu magoya bayansa sun bude ofishin yakin neman zabensa a jihar Osun.

Duk magoya bayansa sun bude ofishin yakin neman zaben, Tinubu bai taba fito wa ya bayyana wa jama'a a cewa zai yi takarar shugaban kasa ba a shekarar 2023.

An bude ofishin yakin neman zaben ne a Osogbo, babban birnin jihar Osun, kuma an kafa babban allon takarar Tinubu a sakatariyar.

An rubuta "Tinubu 2023" baro-baro a jikin allon tallar tare da kara yin rubutu cikin harshen turanci da ke nuna suna da muradin kungiyar da suka bude ofishin; 'Tinubu is Non Negotiable, (TNN 2023)', wanda za a iya fassara shi a Hausa da cewa Tinubu ba zai fasa takara ba a shekarar 2023.

DUBA WANNAN: Zaben Nuwamba: Tsohon mataimakin gwamna da jiga-jigan 'ya'yan PDP sun fice daga jam'iyyar a Bayelsa

An yi amfani da ginin da aka bude ofishin wajen yakin neman zaben tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Osun, Honarabul Najeem Salaam, yayin zaben gwamnan jihar da aka yi a shekarar da ta gabata.

An cire fastocin tsohon shugaban majalisar daga ginin tun bayan lokacin da ya janye wa gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, takara.

Ofishin da kallon gidan Oranmiyan, ofishin tsohon gwamnan jihar Osun, Mista Rauf Aregbesola, da ke kan hanyar Gbongan zuwa Ibadan a garin Osogbo.

Wani mutum mai suna Honarabul Mutiu Kunle Okunola shine wanda ya dauki nauyin allon tallar Tinubu da aka kafa a sabon ofishin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel