'Yan Najeriya 173 sun dawo daga kasar Libya

'Yan Najeriya 173 sun dawo daga kasar Libya

Hukumar NEMA mai kula da bayar da agajin gaggawa ta Najeriya tare da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai wato EU, sun sake yakito wani kaso na al'ummar Najeriya daga da suka tafi cirani Kasar Libya.

Jami'in Hukumar NEMA reshen Kudu maso Yamma na Najeriya, Alhaji Abubakar Muhammed, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a jihar Legas.

Alhaji Abubakar ya bayyana cewa, cibiyar hijira ta duniya wato IOM (International Organisation for Migration) ce ta sake bayar da tallafin yakito wannan kaso na 'yan Najeriya 173 daga Kasar Libya da suka tafi cirani.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, baƙin hauren har kashi biyu sun sauka a farfajiyar jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Muhammad da ke birnin Ikkon Legas.

KARANTA KUMA: Furuci 10 da bai kamata miji ya yi wa matarsa ba

Ya kara da cewa, wannan sabbin kaso na baƙin haure da aka yaso daga Kasar Libya sun dawo Kasar su ta gado ne bisa ga ra'ayi a yayin da cibiyar ta IOM ta basu dama ta tallafin jigilar su zuwa Najeriya.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, a bisa tafarki na bin kundin tsarin kungiyar ECOWAS mai bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, kasar Nijar ta haramta shigo da shinkafa zuwa Najeriya biyo bayan hukuncin da gwamnatin kasar ta zartar na rufe iyakokinta da ke tudu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel