Gwamnatin Tarayya ta ware wa 'yan Matan Chibok N360m domin karatu a jami'ar Atiku

Gwamnatin Tarayya ta ware wa 'yan Matan Chibok N360m domin karatu a jami'ar Atiku

Ma'aikatar kula da harkokin Mata ta gwamnatin tarayya, ta ce ta ware Naira miliyan 360 domin tanadin harkokin karatun wasu daga cikin 'yan Matan Chibok da aka ceto a hannun kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa a rahoton ranar 14 ga watan Oktoban 2019, tanadin da gwamnati ta yi na nufin an ware wa kowace daya daga cikin 'yan Matan 106 Naira miliyan 3.3 domin dawainiyar karatunsu.

Sanarwar hakan na kunshe cikin daftarin kasafin kudin kasa na 2020 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a gaban majalisun tarayya a ranar Talata ta makon jiya.

A halin yanzu 'yan Chibok 106 da suka kubuta daga hannun 'yan Boko Haram na ci gaba da halartar jami'ar American University, da birnin Yola, wadda ta kasance mallakin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar.

KARANTA KUMA: Dattawan Kano sun bayyana damuwa kan yaran da aka ceto daga hannun masu safarar mutane a jihar Anambra

Kididdigar alkalumma ta tabbatar da cewa, Naira miliyan 360 da ma'aikatar kula da harkokin mata ta kasa ta ware domin daukar nauyin karatun 'yan matan, ya kasance kaso 9 cikin 100 na naira biliyan 3.9 da ma'aikatar za ta batar a badi.

Ana iya tuna cewa, a ranar Talatar da gabata ne shugaban kasa Buhari ya gabatar da kudurin kasafin 2020 na Naira tiriliyan 10.729 ga zaman hadin gwiwa da ya kunshi mambobin majalisun tarayya biyu na wakilai da kuma dattawa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel