Kasar Nijar ta haramta shigowar shinkafa zuwa Najeriya

Kasar Nijar ta haramta shigowar shinkafa zuwa Najeriya

A bisa tafarki na bin kundin tsarin kungiyar ECOWAS mai bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, kasar Nijar ta haramta shigo da shinkafa zuwa Najeriya biyo bayan hukuncin da gwamnatin kasar ta zartar na rufe iyakokinta da ke tudu.

Ana iya tuna cewa, tun a ranar 20 ga watan Agsutan 2019 ne gwamnan Najeriya ta rufe iyakokinta na kan tudu da ke yankunan kasar hudu da suka hadar; Kudancin Kudu, Kudu maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa ta Yamma.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, gwamnatin kasar Nijar ta dauke wannan mataki na haramta shigo da shinkafa biyo bayan hukucin da gwamnatin Najeriya ta dauka na rufe iyakokinta da ke tudu da manufa haramta shigowa kayayyakin fasa-kwauri domin bunkasa tattalin arziki.

Wannan sanarwa ta fito daga bakin shugaban hukumar hana fasa kwauri na kasa, Kanal Hameed Ali, yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin cikin birnin Abuja. Ya ce a bayan nan ne kasar Nijar ta haramta shigo da shinkafa Najeriya sanadiyar rufe iyakokin kan tudu na kasar.

KARANTA KUMA: Wacece Sadiya Umar Farouq, matar da ake rade-radin Buhari zai aura

Kanal Ali ya ce za a ci gaba rufe iyokokin kasar da ke tudu har zuwa lokacin da Najeriya za ta samu cikakken hadin kai daga sauran kasashen da take makwabtaka da su.

Yayin zayyana dalilin wannan mataki da hukumar hana fasa kwaurin kasar nan ta daukta bisa lamuncewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce tun a yanzu kafin aje ko ina, harkokin tsaro da na tattalin arziki sun soma inganta, lamarin da ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu kenan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel