Bayan biyan kudin fansan N5m, an sako mutane 8 da aka sace a Abuja

Bayan biyan kudin fansan N5m, an sako mutane 8 da aka sace a Abuja

An sako mutane takwas cikin goma da aka sace ranar Litinin da ya gabata a unguwar Pegi, karamar hukumar Kuje a birnin tarayya Abuja.

Bayan roko da lallashi, an samu labarin cewa an sako mutanen ne sun yi aman milyan biyar na fansa. The Naton ta bada rahoto.

A cewar majiya, masu garkuwa da mutanen sun ci mutuncin mutanen kan gazawar iyalansu wajen biyan kudin fansan da suka bukata.

Wani mazaunin Kuje wanda aka sakaye sunansa ya ce a ranar Lahadi aka saki mutum na takwas.

Ya ce har yanzu akwai akwai mutane biyu a hannun masu garkuwa da mutanen.

Ya ce daya daga cikin mutanen da aka sace, AbdulMajeed Dayo, ya kai ziyara ne wajen abokinsa inda akayi awon gaba da shi da mai babur din da ya daukesa.

KU KARANTA: Daga samun labarin mutuwan matarsa, wani fasinja ya yanke jiki ya fadi a filin jirgin Legas

Majiyar tace: "An saki Dayi a ranar Juma'a bayan kwashe kwanaki biyar wajen yan garkuwan. Ya ce sun hanasu abinci kuma su kan doki suk wanda iyalansa suka gaza kawo kudin fansan da aka bukata."

"Dayo ya kara da cewa iyalan mai babur din da aka sace sun biya fiye da N500,000 kafin masu garkuwa da mutanen suka j tausayinsa suka karba. Sauran sun biya fiye da hakan kuma sun tara sama da milyan biyar."

Tabbatar da sakinsu, shugaban kungiyar cigabar unguwar Pegi, Mista Isaac Taiwo, ya ce lallai ya ga wadanda aka sacen sun dawo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel