Na tafi Ingila jinya ne - Aisha Buhari

Na tafi Ingila jinya ne - Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi bayanin cewa ta kwashe watanni biyu a kasar Ingila ne saboda jinya bisa ga shawarar likitanta.

Aisha, wacce ta isa babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja misalin karfe 5 na Asuba ta ce bayan fara jinya a Ingila, sai ta tafi aikin Hajji a Saudiyya sannan ta sake komawa Ingila bisa shawaran likitanta.

Rashin kasancewarta a gida ya tayar da jita-jitan cewa mijinta, shugaba Muhammadu Buhari, na shirin auren ministarsa. Sadiya Umar Farouq, a ranar Juma'ar da ya gabata.

Ta ce duk da cewa ta samu lafiya yanzu, ta na bukatar lokaci domin hutawa kuma ta mika godiyarta ga mijinta wanda ya nada mata hadimai shida.

Tace:"A shekarar da ya gabata, na kwashe watanni biyu a kasar Andalus tare da diyata. Bana share 'yayana, ina kula dasu a matsayin uwa. A al'ada, mukan je hutu kowani shekara na makonni shida."

"Ya faru cewa bayan hutuna, na bukaci kula da lafiyana kafin zuwa kasar Saudiyya. Bayan zuwa Saudiyya, na koma Ingila bisa umarnin Likita."

Akan dalilin da yasa ta dade a kasar waje, hadimarta ta musamman akan yada labarai, Olabisi Olumide-Ajayi ta ce: “Tun kafin hawan shugaban kasar karagar kujerar mulkin kasar nan, al’adarta ce zuwa dogon hutu tare da ‘ya’yanta kasar waje. Amma tunda ya hau mulkin, hakan bai samu ba saboda aiyuka basu barta ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel