Zaben Nuwamba: Tsohon mataimakin gwamna da jiga-jigan 'ya'yan PDP sun fice daga jam'iyyar a Bayelsa

Zaben Nuwamba: Tsohon mataimakin gwamna da jiga-jigan 'ya'yan PDP sun fice daga jam'iyyar a Bayelsa

Tsohon mataimakin gwamna a Bayelsa kuma jigo a PDP a jihar, Ebeb Peremobowei, ya yi murabus daga zama mamba a jam'iyyar a yayin da zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba ke kara matso wa.

Ebebi, tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Bayelsa, ya aika takardar yin murabus daga PDP ga shugaban jam'iyyar na mazaba ta uku da ke Alaebiri a yankin karamar hukumar Ekeremor.

Masu ruwa da tsaki a PDP sun bayyana ficewar Ebebi daga jam'iyyar a matsayin babbar damuwa, musamman a daidai lokacin da aka nada shi a matsayin jagoran yakin neman zaben jam'iyyar PDP a yankin yammacin jihar Bayelsa.

Sai dai, wasu rahotannin da ke fitowa daga Bayelsa na nuni da cewa gwamnan jihar, Seriake Dickson, ya tuntubi tsohon mataimakin gwamnan inda ya tabbatar masa da cewa jita-jitar ficrewarsa daga jam'iyyar ba gaskiya bane.

Amma a cikin wasikar da Ebebi ya aika wa shugaban mazabar, ya ce ya yanke shawarar fita daga PDP ne bayan ya gaji da jure siyasar kama karya da ake yi a cikin jam'iyyar a jihar.

DUBA WANNAN: 2023: An bude ofishin yakin neman zaben Tinubu a jihar kudancin Najeriya

Kazalika, wasu daga cikin masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin jihar Bayelsa a karkashin jagorancin Dickson sun ajiye mukamansu a yayin da PDP ke gudanar da shirye-shiryen fara neman yakin neman zaben gwamna a jihar.

A ranar Alhamis ne wasu hadiman gwamna Dickson guda biyu; Benjamin Ogbara da Cif Natus Zebakame, sun mika takardunsu na ajiye aiki.

Sauran wadanda suka ajiye mukaman nasu sune; Godspower, Ake mai rike da mukamin kwamishina, Berry Negerese, Iniruo Ipogi da Clever Ebede da sauransu.

Amma shugaban jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa, Cif Moses Cleopas, ya ce jama'ar jihar Bayelsa basa tare da wadanda suka canja shekar tare da bayyana cewa jam'iyyar PDP zata ci zaben gwamnan da za a yi duk da sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel