Maraba da Ganduje: Sarki Sanusi ya tube rawanin wani babban basarake a fadarsa

Maraba da Ganduje: Sarki Sanusi ya tube rawanin wani babban basarake a fadarsa

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayi umurnin sallaman Maja Siddin Sarkin Kano, Alhaji Auwalu akan shiga sahun masu bikin maraba da Gwamna Abdullahi Ganduje a ranar Laraba da ya gabata.

An kuma bukaci Maja Sidden Sarkin Kano, wanda ke kula da kawata dokin Sarkin, da ya tashi daga gidansa wanda ya shafe shekara 30 a ciki.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa lamarin ya haifar da tashin hankali sosai a majalisar sarkin Kano.

Alhaji Auwalu ya fara shiga matsala ne lokacin da ya daga hoton marigayi sarkin Kano, Mai martaba, Sarki Ado Abdullahi Bayero domin taya Ganduje murna yayinda dogon ayarin motocin gwamnan suke wucewa ta fadar sarki daga filin jirgin sama na Kano zuwa gidan gwamnati a ranar Laraba da ya gabata.

Wata majiya ta fadar sarki wacce ta nemi a boye sunan ta, tace abunda Auwalu yayi ya matukar bata ran sarki Sanusi wanda baya a Kano a lokacin dawowar Ganduje.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kwato wasu yara 8 da aka sayar a Anambra bayan an sace su a Kano

A cewar majiyar hakan da yayi kamar rashin biyayya ne ga sarkin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel