Za a tafi yaji a kan batun sabon karin albashi idan aka saba yarjejeniya

Za a tafi yaji a kan batun sabon karin albashi idan aka saba yarjejeniya

Kungiyar ‘yan kwadagon Najeriya na NLC sun aika wasika ga shugabannin reshen jihohi cewa su fara shirin zuwa yajin aikin din-din-din muddin gwamnatin tarayya ta ki amincewa da bukatunta.

‘Yan kwadagon za su shiga dogon yajin aiki ne wannan karo muddin gwamnatin tarayya ta ki yin na’am da bukatunta zuwa Ranar Oktoba 16. Wannan zai kama ne a Ranar Larabar da ke zuwa.

Yarjejeniyar farko da ake yi tsakanin gwamnatin Najeriya da wakilan ‘yan kwadagon ya ruguje ne bayan da aka gaza cin ma matsaya kan karin albashin da za a yi wa manyan ma’aikatan kasar.

A Ranar Talata 15 ga Oktoba na 2019 ne ma’aikatan za su yi zama da gwamnati. ‘Yan kwadagon su na neman ayi wa manyan ma’aikatan da ke kan rukuni na 07 zuwa 14 karin 29% na albashi.

Haka zalika bangaren kungiyar TUC a madadin ‘yan kwadagon su na so gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi wa ma’ikatan da ke kan rukuni na 15, 16 da kuma 17 karin kashi 24%.

KU KARANTA: Babu maganar angwancewa Shugaba Buhari a Najeriya

Gwamnatin tarayya a na ta bangaren ta kafe ne a kan karin 11% da 6.5% ga ma’aikatan. Wannan ne ya jawo ma’aikatan su ke barazanar tafiya yajin aikin da babu ranar dawowa a fadin Najeriya.

A takardar da shugabannin TUC, da NLC da kwamitocin da ke zama da gwamnati su ka fitar dazu, sun ce da zarar an gaza cin ma matsaya daga Ranar Talata, a shiga yajin aiki babu kaukautawa.

“Ana sanar da ku cewa ku fara harama da TUC da JPSNC na jihohinku kan shirin yajin aiki da zarar lokacin da aka yi alkawari ya wuce ba tare da an cin ma yarjejeniyar da aka tsara ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel