'Yan sanda sun kwato wasu yara 8 da aka sayar a Anambra bayan an sace su a Kano

'Yan sanda sun kwato wasu yara 8 da aka sayar a Anambra bayan an sace su a Kano

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano sun kubutar da wasu yara takwas da aka sace a unguwannin cikin birnin Kano.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an sace yaran ne a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2019, kuma an gano su ne a jihar Anambra, inda aka sayar da su.

Da yake bajakolin masu laifin a gaban manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ahmed Iliyasu, ya ce asirin masu sace yaran ya tonu ne bayan an kama wani mai suna Paul Owne yayin da yake kokarin sace wani mai suna Haruna Bako domin tafiya da shi zuwa jihar Anambra, inda zai sayar da shi.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce an sace Bako ne a ranar 11 ga watan Satumba yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga makarantar Islamiyya a unguwar Yankaba da ke cikin garin Kano.

"Mun saka jami'an mu na rundunar atisayen 'Puff Adder' gudanar da binciken kwakwaf a kan mai laifin da aka kama domin gano sauran abokan muguwar sana'arsa.

DUBA WANNAN: Yunusa Ado: Hukumar DSS ta yi magana bayan sakin kasurgumin dan damfara a Kano

"Ragowar abokansa da jami'an mu suka kamo sun amsa cewar suna satar yara a unguwannin cikin birnin Kano irinsu Sauna, Kwanar Jaba, Kawo, Hotoro, 'Yan kaba da Dakata," a cewar kwamishinan.

Kazalika, kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa wani mutum mai suna Sagir Bako ya taba shigar da korafin cewa ana sace kanan yara da basu wuce shekaru shida ba tare da tafiya da su zuwa wuraren da babu wanda ya sani.

Daga cikin masu sace yaran da aka kama akwai; Paul Owne, Mercy Paul, Emmanuel Igwe, Ebere Ogbodo, Louisa Duru da Monica Orachaa.

Iliyasu ya ce an sada yaran da aka kwato da iyalinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel