Yunusa Ado: Hukumar DSS ta yi magana bayan sakin kasurgumin dan damfara a Kano

Yunusa Ado: Hukumar DSS ta yi magana bayan sakin kasurgumin dan damfara a Kano

Hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) reshen jihar Kano, ta musanta zarginsu da ake yi da sakin Yunusa Ado da ake zargi da damfarar jama'ar naira miliyan 18.

A makon da ya gabata ne hukumar jami'an tsaron ta farin kaya ta kama Yunusa bayan samun bayanan sirri a kan al'amuransa. Hukumar ta mikashi ga babbar kotun majistare da lamba 72 Normansland inda aka aje shi a gidan maza.

Babban jami'in hukumar wanda ya zanta da jaridar Solacebase a Kano kuma ya bukaci a boye sunansa, ya ce, "A matsayin mu na jami'ai, muna aikinmu na cafke wadanda ake zargi da damfara kuma mu mikasu ga kotu, wanda hakkin alkali ne ya sake su ko yasa a ajiye su a gidan yari ko kuma ya bayar da belinsu".

"Amma kuma abin mamaki, sai aka ga Yunusa na yawo hankali kwance a daren da muka kama shi, hakan na nuna cewa alkalin kotun da aka gurfanar da shi ne ya bada belinsa", in ji jami'in.

Ana zargin Yunusa Ado ne da sanya yaransa yi wa jama'a rijista da sunan zai sama musu gurbi a shirin N-Poverty, inda suke karbar N30,000 zuwa N50,000 daga kowanne mutum. An gano cewa ya yi wa mutane sama da 5,000 irin wannan rijistar bogin.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP mai matsayin Farfesa ya koma jami'a domin yin digiri a kan Shari'a

Bayan samun makuden kudade daga damfarar da ya yi, Yunusa Ado ya siyawa mahaifiyarsa gida na naira miliyan shida a cikin Kano.

Wata majiyar a cikin jami'an farin kayan ta ce, Yunusa ya amsa laifukansa a gaban kotu inda ya roki yafiya tare da alkawarin zai maidawa wadanda ya damfara kudadensu.

Kamar yadda majiyar ta sanar, " Daga nan ne alkali ya bukaci a ajiyeshi a gidan maza tare da dage shari'ar zuwa Talata mai zuwa. Amma abin mamaki sai aka ganshi yana yawo a gari. Bazamu iya tambayar alkalin ba, amma babu hannunmu a ciki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel