Abin da Aisha Buhari ta fada bayan dawowar ta Najeriya

Abin da Aisha Buhari ta fada bayan dawowar ta Najeriya

A ranar Lahadi, 13 ga watan Satumba, Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta dawo gida Najeriya bayan ta shafe lokaci mai tsawo ba ta kasa.

A cewar wani jawabi da kakakinta, Suleiman Haruna, ya fitar, ya ce Aisha Buhari ta sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 4:30 na safe.

Aisha ta ce ta yi murnar dawowa gida Najeriya bayan shafe lokaci mai tsawo tana hutawa a kasashen ketare.

Aisha ta samu tarba daga wurin matan tsofin gwamnoni da masu ci a yanzu da kuma wasu kawaye, hadimai da 'yan uwa.

"A safiyar nan matar shugaban kasa, Dakta Aisha Muhammadu Buhari, ta dawo gida Najeriya bayan ta sha dogon hutu a kasar Ingila.

"Ta sauka a filin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a jirgin 'Bristish Airways' da misalin karfe 4:30 na safe," a cewar jawabin.

DUBA WANNAN: Tikar rawa da mace: Sheikh Daurawa ya magantu a kan bullar wani faifan bidiyo da ake zaton shine ke cashe wa tare da matarsa

Da take magana da manema labarai jim kadan bayan saukar ta a filin jirgin, Aisha ta bayyana cewa ta yi farincikin dawowa gida bayan ta sha dogon hutu.

Jawabin ya kara da cewa, "uwargidan shugaban kasa ta tabbatar da cewa ta samu karin karsashi yayin hutun da ta sha tare da bayar da tabbacin cewa za ta cigaba da aiki tukuru wajen inganta lafiyar mata, yara da sauran 'yan Najeriya masu karamin karfi."

Dadewar da Aisha ta yi a kasar Ingila ya jawo cece-kuce da kace-nace a tsakanin 'yan Najeriya. Zance ya gama karada Najeriya cewa Aisha ta yi yaji ne saboda shugaba Buhari na shirin kara auren mata ta biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel