A wannan shekarun nawa, wa zai ce na yi kyau? – Buhari ga Ramaphosa (Bidiyo)

A wannan shekarun nawa, wa zai ce na yi kyau? – Buhari ga Ramaphosa (Bidiyo)

A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Tawagarsa su kai ziyarci kasar Afrika ta Kudu bayan wasu munanan hare-haren da aka rika kai wa bakaken baki a kasar.

Kafin shugaban kasar na Najeriya ya baro kasar, sun yi wata liyafa da shugaba Cyril Ramaphosa inda ya fadi wani abu da ya ba mutanen da ke tare da su dariya a wajen wannan zama.

Tolu Ogunlesi wanda ya na cikin Masu taimakawa shugaban kasa Buhari a kan harkokin yada labarai a yanar gizo, shi ne ya fitar da wannan bidiyo na tattaunawar Buhari da Takawaran na sa.

Za a ji shugaba Cyril Ramaphosa ya na nunawa Buhari hotunan da aka dauke sa ne a zuwansa kasar ta Afrika ta Kudu inda ya yi kokarin yaba masa da cewa hotunan sun yi matukar kyau.

Nan take Mai girma shugaba Muhammadu Buhari mai neman cika shekara 77 ya maidawa Ramaphosa martani da cewa a wannan shekarun na sa ne za ayi maganar kyawunsa a cikin hoto.

KU KARANTA: Buhari zai sallami masu kamfanin wutan Yola idan an sa hannu a kasafin 2020

Wannan ya sa kusan kowa da kewayen shugabannin ya fashe da dariya a wajen cin abincin. Shugaban kasa Buhari yake cewa abin da ya kamata a fada shi ne, a shekarun baya ya na da kyau.

Shugaba Ramaphosa na Afrika ta Kudu yayi na’am da shugaban na Najeriya a kan wannan inda yace babu shakka a zamanin da Buhari kyakkyawan siririn mutum ne kuma ‘dan Dogon Matashi.

A wannan takaitaccen bidiyo da Mista Ogunlesi ya wallafa a Ranar 7 ga Okotoba a Tuwita, za a hangi wata Mace mai shekaru da wani Namiji guda a gefen shugabannin kasashen Afrikan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel