EFCC ta mallakawa gwamna AbdulRazaq N111.4m da ta kwato a hannun barayin gwamnatin jihar Kwara

EFCC ta mallakawa gwamna AbdulRazaq N111.4m da ta kwato a hannun barayin gwamnatin jihar Kwara

A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta mallakawa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, Naira miliyan 111.4 da ta kwato a hannun barayin gwamnatin jiharsa.

Shugaban EFCC reshen jihar, Isyaku Sharu, shi ne ya gabatar da wannan zunzurutun kudi cikin rubutacciyar takardar banki zuwa ga gwamnan a fadarsa da ke birnin Ilorin. Sharu ya ce an kwato kudaden ne daga hannun wadanda suka rinka tatsar baitul malin jihar Kwara.

Sharu ya ce hukumar ya zuwa yanzu ta samu nasarar kwato kimanin Naira miliyan 500 na kadarori da kuma tsabar kuɗi daga hannun mazambatan kudaden talakawa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, cikin wadanda hukumar EFCC ta kwato dukiyar da suka tatsa daga lalitar gwamnatin jihar sun hadar da masu rike da madafan iko na siyasa, sarakunan gargajiya da kuma manyan ma'aikatan gwamnati.

KARANTA KUMA: Haraji: Jihohin Najeriya 36 da Abuja sun tara N691.11bn a watanni 6 na shekarar 2019 - NBS

Gwamna AbdulRazaq bayan yabo da kuma jinjina, ya yai godiya ga Hukumar EFCCC tare da cewa gwamnatinsa za ta ribaci wannan kudade da aka mallamka mata wajen ci gaba da shirye-shiryen bayar da tallafi ga al'umma domin yaye katutu na talauci a jihar.

Ya kara da cewa, ko kadan gwamnatinsa ba za ta ribaci wannan kudade wajen gudanar da wani aiki ba a jihar face hanyoyin na rage wa al'ummar jihar radadin talauci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel