Bayelsa: Yaran Lokpobiri da Sylva sun ja daga a Jam’iyyar APC

Bayelsa: Yaran Lokpobiri da Sylva sun ja daga a Jam’iyyar APC

An samu ‘Yan taware a cikin tafiyar jam’iyyar APC mai neman mulkin gwamna a Bayelsa inda wasu bangare ke tare da Timipre Sylva, yayin da wasu ke goyon bayan Heineken Lokpobiri.

Wannan rikicin cikin gida ne ya jawo wadanda ke tare da tsohon gwamna kuma Ministan man fetur, Timipre Sylva su ka dakatar da wasu Magoya bayan tsohon Minista Heineken Lokpobiri.

Wanda aka dakatar daga jam’iyyar sun hada da shi kansa shugaban APC na jihar, Jonathan Amos da Sakatarensa Alabo Martins da kuma wasu mutane 10 da zargin yi wa jam’iyya zagon-kasa.

Bayan wanan mataki da wasu ‘Ya ‘yan jam’iyyar su ka dauka, an kuma samu dayan bangaren na Jonathan Amos da su ka fito su ka rusa wannan dakatarwa tare da dakatar da ‘Yan hamyyarsu.

KU KARANTA: Jami'in INEC da ya ajiye aiki ya fado ta kai a zaben Bayelsa

Daga cikin wadanda Amos da mutanensa su ka fatattaka daga jam’iyyar, akwai mataimakinsa watau Ogeibiri Orubebe tare da wasu ‘Yan tafiyarsa mutane 7 da ke bayan Heineken Lokpobiri.

Lokpobiri wanda ya yi takarar tikitin APC ya sha kashi a hannun David Lyon, ya garzaya kotu ne inda ya ke kabulantar nasarar Abokin adawar ta sa wanda wasu ke yi wa kallon yaron Sylva.

Wadanda aka dakatar tare da mataimakin jam’iyyar APC a taron da aka yi a makon da ya gabata su ne; Chris Toborowei Olorogun; Ekeremor Amasighan Azikiwe; da Olorogun Isaac Peter Bofini.

Sauran ‘Yan bangaren shugaba Amos da ake takun-saka da su, sun hada da Martins Alabo, Peres Oyadongha, John Williams, Osadebe Ezinrin, Lovely Agwor, da wasu manyan APC a jihar Kudun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel