Kasafin kudi: Gwamnatin Tarayya za ta kashe Biliyan 9.05 a kan Janareta da Mai

Kasafin kudi: Gwamnatin Tarayya za ta kashe Biliyan 9.05 a kan Janareta da Mai

Najeriya ta na shirin batar da Naira biliyan 9.05 domin sayen na’urorin bada wutar lantarki da kuma gyaran sauran na’urorin da ke kasa. Za kuma a kashe makudan kudi wajen sayen mai.

Kasafin kudin shekarar 2020 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a gaban majalisa a Ranar Talata 8 ga Watan Oktoban 2019 ya nuna cewa an warewa na’urori wannan biliyoyi.

Bayan sama da biliyan da aka warewa sababbin na’urorin na Janareta, an kuma kasafta wasu miliyan 75.4 da za a kashe a ofisoshin wasu Jakadun Najeriya da ke kasar waje a shekarar badin.

Rahotannin da su ka zo daga jaridun Najeriya sun nuna cewa abin da gwamnatin tarayya za ta kashe wajen ganin samun wutar lantarki a shekara mai zuwa zai haura wadannan biliyoyin kudi.

KU KARANTA: Za a biya masu kamfanin wutan Yola idan an sa hannu a kasafin 2020

Hakan na zuwa ne bayan sauran manyan hukumomin kasar irinsu INEC mai gudanar zabe da kuma NHIS sun ki bayyana ainihin abin da ke cikin kundin kasafin kudinsu na shekarar 2020.

Gwamnatin shugaba Buhari ta na ikirarin cewa ta inganta wutar lantarki a kasar. Duk da wannan, gwamnati ta na cigaba da batar da makukun kudi wajen ganin ma’aikatu sun samu damar aiki.

Abin da aka warewa na’urorin da za a saya daga kasashen ketare ya haura irin kudin da gwamnatocin jihohi sama da 15 su ka iya tatsowa da kansu a cikin tsakiyar shekarar nan ta bana.

Sojojin Najeriya ne za su fi kowa kashe kudi wajen sayen na’urorin wutar lantarki. Masu bin su a baya su ne hukumar EFCC. Irin su makarantar NDA da kwalejin ‘yan sanda da NIS su ne a biye.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel