Dalilin da yasa na dade a kasar waje - Aisha Buhari

Dalilin da yasa na dade a kasar waje - Aisha Buhari

- A safiyar yau ne uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta sauka kasar nan bayan kusan watanni uku da tayi bata kasar

- Ta bayyana cewa, al'adarta ce tafiya dogon hutu tare da 'ya'yanta kasar waje

- Ta dawo gida inda ta samu tarbar dangi da abokan arziki

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bada dalilan da suka sa ta dade a kasar waje.

Ta yi maganar ne bayata an da ta dawo kasar wajen karfe 4:30 na safiyar yau Lahadi.

Akan dalilin da yasa ta dade a kasar waje, mataimakiyarta ta musamman akan yada labarai, Olabisi Olumide-Ajayi ta ce: “Tun kafin hawan shugaban kasar karagar kujerar mulkin kasar nan, al’adarta ce zuwa dogon hutu tare da ‘ya’yanta kasar waje. Amma tunda ya hau mulkin, hakan bai samu ba saboda aiyuka basu barta ba.”

KU KARANTA: Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta dakatar da rubuta jarabawar malamai a jihar Ibadan

Tace a shiye take don cigaba da aiyukanta tare da mata da kananan yara.

Wadanda suka tarbeta a filin jirgin sun hada da: Rasheedat Bello; matar gwamnan jihar Kogi, Mairo Al Makura; matar tsohon gwamna jihar Nassarawa, Ekaetae Unoma Godswill Akpabio; matar ministan al’amuran Niger Delta, Mary Etta; shugabar cibiyar habaka mata da Dr Hajo Sani; babbar mataimakiya ta musamman ga ofishin uwargidan shugaban kasan.

Ta isa fadar shugaban kasar inda ta iske iyalai da abokan arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel